Babban editan Sashen Hausa na Muryar Amurka Aliyu Mustapha ya samu ya yi fira da shugaban Najeriya Muhammad Buhari inda suka tabo batutuwa da dama.
Da farko dai shugaba Buhari ya ce shugaban Amurka ne ya gayyaceshi shi kuma ya amince, Allah kuma cikin ikonsa ya bashi zarafin zuwa.
Shugaban Najeriya ya ce shugabannin Amurka sun soma fahimtar mahimmancin Najeriya a nahiyar Afirka da duniya gaba daya.
Tun kafin Donald Trump ya karbi mulki Najeriya ta nemi sayen jiragen yaki amma gwamnatin Obama bisa wasu dalilai ta ki. Haka ma wasu kasashen dake da jiragen suka ce ba zasu sayarwa Najeriya ba sai da izinin Amurka. Amma da Shugaba Trump ya kama mulki ya kira shugaban Najeriya ya nemi kudin sayen jiragen zai yadda a sayarwa Najeriya.
A tattaunarwasa da Shugaba Trump, shugaba Buhari ya ce sun tabo batun kashe-kashen da ake yi a Najeriya har da zargin cewa ana kashe Kiristoci. Shugaba Buhari ya ce ya bayyyana abubuwan dake faruwa a duk fadin kasar domin kawar da wannan zargin. Shugaba Buhari ya ce isgili ne a keyi a ce Makiyaya na kashe Tibi ko mabiya wani addini a Buniwai ko Taraba. Ya ce kashe kashen da a keyi a Zamfara ya fi na Binuwai ko Taraba.
Dangane da matakan tsaro Shugaba Buhari ya ce ya bada umurnin a kara 'yan sanda dubu shida amma a je kowace karamar hukuma a dauki mutane. Akan barin jihohi su kafa nasu 'yan sadan hankalin shugaban bai kwanta a yi ba sai idan an kawar da ta'addanci kuma an tabbatar jihohin zasu iya biyan albashin 'yan sandan.
Ku saurari firar Shugaba Buhari da Aliyu Mustapha
Facebook Forum