WASHINGTON, D. C. - Pakistan za ta kada kuri'a a ranar Alhamis 8 ga watan Fabrairu; a daidai lokacin da ake samun karuwar hare-haren 'yan bindiga a cikin 'yan watannin nan da kuma tsare Imran Khan, wanda ya lashe zaben kasar da ya gabata, wanda ya mamaye kanun labarai duk da rikicin tattalin arziki da wasu matsaloli da ke barazana ga kasar mai makaman nukiliya.
Hukumomin kasar dai sun ce suna karfafa matakan tsaro a rumfunan zabe. Harin farko wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 14, an kai shi ne a ofishin ‘dan takarar zabe mai zaman kansa a gundumar Pishin.
Fashewar na biyu a garin Qila Saifullah da ke kusa da kan iyaka da Afganistan ya tarwatse ne a kusa da ofishin Jamiat Ulema Islam (JUI), jam'iyyar addini da a baya ta sha kai hare-hare kamar yadda ministan yada labaran lardin ya bayyana.
Mataimakin kwamishinan Qila Saifullah, Yasir Bazai ya ce mutane 12 ne suka mutu sakamakon fashewar bam din da ta samo asali daga wani babur da aka ajiye a kusa da ofishin, sannan 25 suka jikkata.
Kawo yanzu dai ba a bayyana ko su waye suka kai hare-haren ba.
-Reuters