Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Wata Fashewa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutum 17 A Ghana


Lokacin da wata tankar mai ta fashe a Accra Ghana a shekarar 2017.
Lokacin da wata tankar mai ta fashe a Accra Ghana a shekarar 2017.

Bayanai sun yi nuni da cewa a lokacin da hatsarin ya faru direban ya sauka daga motar yana yekuwar mutane sun gudu daga wurin.

Mutane 17 sun mutu sakamakon wata gagarumar fashewa da ta auku a kauyen Apiate kana kusan wasu 40 suka jikkata, a cikin gundumar Prestea Huni-Valley, dake yankin yammain kasar Ghana.

Da yake jawabi ga manema labarai a kan lamarin, Kantomar yankin Dr. Issac Dasmani, ya ce an kai wasu mutane uku Kumasi kana wasu biyu an tura su zuwa asibitin garin Tarkwa, yayin da aka lissafa gawarwaki 17.

Hukumomi sun ce binciken farko ya yi nuni da wata babbar mota dauke da abubuwan fashewa da ake amfani da su wurin hakar ma’adinai da ta fito daga garin Tarkwa zuwa kamfanin Chirano mines ne ta ci karo da wani babur, lamarin da ya kai ga fashewar.

Bayanai sun yi nuni da cewa a lokacin da hatsarin ya faru direban ya sauka daga motar yana ihu yana fadawa jama’a kowa ya bar wurin saboda wuta za ta tashi, amma sai wasu suna so su je ganin abin dake faruwa, bayan mintuna 10 sai wuta ta tashi kuma wadanda suka je kallo ne fashewar ta fi musu lahani har da hallaka wasu.

Ya ce kauyen Apiate baki daya ya rushe har wasu mutane sun mutu a cikin gidajen dake kusa da inda fashewar ta auku kana hukumarsa ta shirya matsuguni na wucin gadi mutanen kauyen a garin Bogoso dake kusa da kauyen wasu kuma dake da ‘yan uwa da abokai a kauyukan dake kusa da wurin sun je wurin domin samun matsuguni.

Dr Dasmani ya kara da cewa ma’aikata na nan na aiki ceto jama’a.

Ya ce ma’aikatan kwana kwana daga Prestea da ma sojoji da kuma ‘yan sanda duka sun kawo dauki ga halin da ake ciki.

‘Yan sandan sun ce suna ci gaba da ba da tsaro domin baiwa ma’aikatan agajin gaggawa dama su gudanar da aikin ceto, da suka hada da ma’aikatar kwan- kwana ta kasa da hukumar kai agaji lokain bal’I ta NADMO da kuma ma’aikatar ambulan.

XS
SM
MD
LG