Duk da kokarin da jami'an kwanwa-kwana ke yi na kashe gobarar daji a jihar California, har yanzu iska na yin barazana a yankin.
WASHINGTON DC —
Raguwar karfin iska da zafin rana sun taimakawa dubban jami’an kwana-kwana a jihar California dake yammacin Amurka a kokarin da suke yi na kashe gobarar daji dabam dabam da suka barke a fadin jihar ranar Lahadin da ta gabata.
Ma’aikatar kula da dazuzzuka da kare gobarar daji dake California ta yi gargadin cewa har yanzu iska da zafi na zama barazana a wuraren, kuma ya zuwa yammacin jiya Talata, gobarar ta kona fiye da hekta 46,500 na fili.
A yau Laraba hukumomi sun bada rahoton mutuwar mutane 17 dake da alaka da gobarar, sun kuma ce gobarar ta kona kimamin gidaje da wuraren kasuwanci ko kuma shaguna 1,500.