Har yanzu dai ‘yan Najeriya na ci gaba da fuskantar barazana saboda wanzuwar matsalolin da ke zama sanadin salwantar rayuka da dama, duk da matakan da a ko da yaushe mahukunta ke cewa suna dauka na magance irin wadannan matsalolin.
A yankin Shagari da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya, wani mummunan hadarin kwale-kwale yayi sanadin mutuwar mutane 15.
Shugaban karamar hukumar Shagari Aliyu Dantanin Shagari, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata da maraice ya kuma tabbatar da mutuwar mutum 15.
Mutun 25 ne a cikin kwale-kwalen da ke kan hanyar zuwa wurin Mauludi a lokacin da hadarin ya faru.
Yankin Shagari ya sha fuskantar wannan matsala ta hadarin kwale-kwale wadda kuma ke zama dalilin mutuwar mutane da dama, abinda ya sa har gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal a wata ziyarar ta'aziyya da ya kai yayi wa al’umar yankin alkawalin samar da riguna masu taimakawa wajen hana nutsewa cikin ruwa idan aka samu irin wannan matsala.
Masharhanta sun sha yin tsokaci akan hadurran kwale-kwale da yadda ya kamata mahukunta da jama'a su sa ido don kaucewa aukuwar matsalar.
Farfesa Bello Badah, mai sharhi akan lamurran yau da kullum, na ganin amfani da tsofaffin kwale-kwale na daga cikin abubuwan da ke haddasa hadarin da kuma yadda ake daukar mutane da kaya fiye da kima.
Ya kuma ce ya kamata mahukunta su sa ido don tabbatar da ana amfani da kwale-kwalen da ya dace da kuma adadin jama’a da kayan da suka dace.
Bayan ayyukan ‘yan ta’adda da kuma hadarin mota a wasu sassan Najeriya, matsalar hadarin kwale-kwale na daga cikin matsalolin da ke lakume rayukan jama’a.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir.
Your browser doesn’t support HTML5