Kanal Sani Usman Kuka Sheka ne ya tabbatar wa manema labarai hakan, wannan tashin boma boman yazo ne makonni biyu bayan tashin wasu boma bomai da aka samu a unguwar Ajilare, wanda ke kusa da unguwar Sajeri inda aka sami tashin bom din na jiya Alhamis.
Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda, ya ziyarci wannan unguwa ta Sajeri dan ganin yadda wannan abubuwa suka wakana ya kuma zanta da ‘daya daga cikin shugabannin ‘yan Gora mai suna Badaru, wanda kuma ya shaidawa wakilin mu cewa shugabansu ma ya tsallake rijiya da baya alokacin da wata ‘yar kunar bakin wake ta tunkareshi da bom a jikin ta.
Baduru dai yace mutanen da ya gani da idonsa sun rasa rayukansu sun kai kimanin goma sha takwas, kuma yara mata ‘yan kasa da shekaru goma sha takwas ne suka kai harin.
Alokacin da wakilin Muryar Amurka ke zatawa Badaru, sai wata mota da ta dauko gawarwakin wasu yara guda takwas da bom din ya hallaka a wannan unguwa ta tsaya. Bayan sauke gawarwakin ne ya ci gaba da zantawa da mutanen unguwar wanda suka ganewa idanunsu yadda lamarin ya wakana, har ma suka shaida masa cewa yanzu haka akwai wani bom din da har yanzu bai tashi ba.
Saurari cikakken rahotan.
Your browser doesn’t support HTML5