Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Bindiga Ya Harbe Mutane 10 a Wata Makaranta nan Amurka


'Yansanda da mutane a harabar makarantar da aka kashe mutane 10
'Yansanda da mutane a harabar makarantar da aka kashe mutane 10

Kashe mutane a makarantu a nan Amurka na neman zama ruwan dare gama gari kamar yadda shugaban kasar kansa ya fada.

Jiya a jihar Oregon dake nan Amurka wani dan bindiga ya shiga wani kwalajin share faggen shiga jami'a inda ya kashe mutane 10 tare da raunata wasu bakwai.

Shugaban kasar Barack Obama wanda ya nuna takaicinsa a fili ya kira amurkawa da su matsawa 'yan majalisar kasar su kafa doka mai tsanani da zata dakile irin kashe kashen ba gaira ba dalili da kasar ke fuskanta.

Shugaba Obama wanda ya bayyana a kafofin talibijan sa'o'i kadan bayan harbin da ya auku ya tunawa jama'ar kasar cewa yawancin amurkawa tare da wadanda suke da bindigogi suna son a yi doka mai tsanani.

Yace lamarin yana kashewa amurkawa jiki saboda yawan kashe kashe dake faruwa a Amurka. Kullum sai a ji an kashe wasu kana fadar White House ta fito ta yi jawabi. Bayan hakan wadanda basa son a kara kafa dokoki da zasu dakile irin wannan haukar sai su fito su yi nasu jawabi na yin adawa da duk wata doka. Kullum nasu matsayin shi ne yawan bindigogi yana kara kare jama'a. Shugaba Obama yace masu fadan hakan sun san ba gaskiya suke fada ba

Shugaba Obama ya kira mau jefa kuri'a su yi la'akari da wadanda basa son a kafa dokokin da zasu taimaka idan sun zo kada kuri'unsu a zabe mai zuwa.

Kawo yanzu ba'a samu cikakken bayani ba akan harbin na Umpqua Community Cllege dake Roseburg jihar Oregon arewa maso yammacin Amurka.

Amma babban jami'in 'yansanda na karamar hukumar Douglas inda makarantar take wato John Hanlin ya tabbatar cewa sun kashe dan bindigan yayinda ya budewa 'yansandan wuta. Halin yace mutumin dan shekarau 20 da haihuwa ya bude wuta ne cikin wani aji amma nan da nan 'yansanda suka isa wurin da suka samu kiran gaggawa.

XS
SM
MD
LG