Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Daukaka Kara Ta Mayarda Sarkin Yamaltu dake Jihar Gombe Kan Mulki


Sanata Muhammadu Danjuma Goje tsohon gwamnan Gombe da ya tsige Sarkin Yamaltu a shekarar 2004
Sanata Muhammadu Danjuma Goje tsohon gwamnan Gombe da ya tsige Sarkin Yamaltu a shekarar 2004

Shekaru goma sha daya da suka gabata gwamnan jihar Gombe na lokacin Danjuma Goje ya tsige sarkin Yamaltu Alhaji Ibrahim Muhammad Bello daga kan mulki.

Jiya kotun daukaka kara ta gwamnatin tarayyar Najeriya ta yanke hukuncin karar dake gabanta inda ta mayarda sarkin Yamaltu Alhaji Ibrahim Muhammad Bello kan karagar mulkin masarautarsa dake jihar Gombe.

An shafe shekaru goma sha daya ana gudanar da shari'a akan shigeshin da aka yi.Barrister Alhassan Aliyu Sange shi ne lauya mai wakiltar sarkin ya kuma kara bayani.

Yace kotun ta ce gwamnatin wancan lokacin a karkashin Danjuma Goje ta kori sarki ne ba tare da wani dalili ba. Saboda haka kotun ta mayar dashi kan mulki. An yi korar ne ba tare da bin tsarin mulkin Najeriya ba . An yi ganin dama ne aka koreshi.

Kotun tace a hada sarkin Yamaltun da na Akko kowannesu ya koma fadarsa. Alkalai uku a karkashin Mai Shari'a Jummai Hannatu Sanke suka yanke hukuncin.

Duk wanda bai gamsu da hukuncin ba na iya daukaka kara zuwa kotun koli.

Dangane da mayarda sarkin Akko lauyan yace suna samun tutsu da tirjiya daga wadansu da suke kusa da gwamnatin jihar Gombe. Yace idan lokaci yayi zai fadi sunayensu kuma zasu dauki matakan da suka dace.

Sarki Ibrahim Muhammad Bello ya godewa Allah da ya bashi nasara a kotun.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG