PLATEAU, NIGERIA - A wata sanarwa daya aikewa manema labarai, kakakin rundunar, DSP Alfred Alabo ya ce gawarwakin mutane goma da suka kone kurmus, an ajiye a mutuware a asibitin kwararru na jihar Filato.
Sanarwar tace motoci uku da keke NAPEP biyu ne suka kone.
Wasu da suka ga yadda hadarin ya auku sun shaida cewa motar dake dankare da man fetur ce ta kwace wa direban ta fadi a kan hanya dake da cinkoson mutane, wanda ya janyo rasa rayuka da jikkatan wadansu mutanen.
Bayan aukuwar hadarin ne matasa suka farma jami’an hukumar kiyaye hadura da ‘yan kwana-kwana da suka zo don yin agaji, bisa cewa basu kawo agaji a kan lokaci ba.
Alhaji Danjuma Khalid, jami’in kungiyar Jama’atu Nasril Islam a jihar Filato ya ce sun kwashe gawarwaki guda goma ya kuma ja kunnen matasa su rika kai zuciya nesa don ba hukumomi sukunin gudanar da aikinsu lokacin da ake neman taimako na gaggawa.
Jami’in hukumar NEMA a shiyyar Arewa ta tsakiya, Nuruddeen Musa ya bukaci gwamnati ta dakatar da tankunan dakon maid daga ratsa cikin gari lokacin da jama’a ke zirga-zirga.
Ana yawan samun haduran manyan motoci a cikin garin Jos musamman saboda hawa da gangara da garin ke dashi, yanayi da al’ummar garin ke fatar gwamnati zata samar musu da mafita.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5