Gobarar ta tashi ne a lokacin da wata babbar tanka ke sauke mai a gidan man AA Rano da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja, kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan birnin Abuja ta fada wa Muryar Amurka.
Tuni dai jami’an kwana-kwana, 'yan sanda, da sauran jami’an ba da agajin gaggawa suka dunguma zuwa gidan man don kashe gobarar.
Amma duk da haka aikin gama ya gama don tankar da ke sauke man ta kone kurmus.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da gobara ke tashi a gidajen mai a birnin ba, lamarin da ke tada hankalin jama’a duba da yadda hakan ke shafar tattalin arziki.