Musulman Ghana Zasu Kama Azumi Gobe ko Jibi

Musulman Ghana zasu fara duban tsayawar watan Ramadan yau Juma'a da nufin kama azumi gobe. Idan basu ga watan ba to wajibi ne su tashi da azumi ranar Lahadi.

Kamar sauran muslman duniya, musulman kasar Ghana ma suna sa idon ganin watan Ramadan yau domin su fara azumi gobe. Idan kuma basu ga wata yau ba sai su tashi da azumi ranar Lahadi.

Biyo bayan taron kwamitin hilal babban jami'i na ofishin shugaban limamin limamai Malam Musa ya bayyana shawarwarin da suka tsayar akan duban watan Ramadan. Yace sun tsayar cewa idan aka ga wata a gunduma za'a kai labari wurin limamin gunduma kana shi kuma ya kai labari ga limamin jiha. Shi limamin jiha zai aikawa limamin limamai na kasar Ghana Shehu Usman Sharubutu wanda zai sanarda kasar ta kafofin gidajen telebijan da na radiyo.

Akan samu cecekuce a duk lokacin da za'a soma duban watan Ramadan. Sheikh Muhammed Haroun daga birnin Kumasi yayi tsokaci akan tsarin da aka shirya. Yace malamai sun zauna sun kuma yi aiki bisa ga sharudan da Manzon Allah ya shimfida. Yace duk wata na mutuwa ne bayan kwana ashirin da tara domin haka Musulmai na iya shirin kama azumi. Ya kira mutane su yi kokari su fita su duba wata.

Ga rahoton Baba Yakubu Makeri.

Your browser doesn’t support HTML5

Musulman Ghana Zasu Kama Azumi Gobe ko Jibi - 3'20"