Asusun tallafawa kasashen duniya kan cututukan sida, tarin fuka, cutar masassarar cizon sauro shi ya kebewa Jamhuriyar Niger kudi dalar Amurka miliyan dari da sittin da hudu ko sefa miliyan dubu saba'in da shida domin yakar cututukan nan da wasu shekaru uku masu zuwa.
Daukacin masu ruwa da tsaki akan cututukan sun hallara a wani gagarumin taro da asusun ya shirya a birnin Niamey domin duba sabbin fasahohin da za'a yi anfani da kudaden da asusun ya kebe domin yin fito- na- fito da cututukan.
Malam Manu Agali ministan kiwon lafiyar Jamhuriyar Niger yayi karin bayani. Yace an kira taron ne domin a yi shirin yadda za'a kashe kudaden ta hanyar da ta dace. Sai an fadakar da kowa da kowa har da ma kafofin labarai kafin a soma yin komi. Mutanen kasa su taru su yi shawara tare da juna akan yadda za'a gudanar da yakin.
Mukaddashin firayim ministan kasar Malam Ladan Chana wanda ya jagoranci bude taron yace kasar ta Niger na baya kwarai akan kula da cututuka kamar su sida da cutar cizon sauro. Tallafawa gwamnati da taimakon masu hannu da shuni nada mahimmanci wajen kauracewa cututukan wadanda suka kasance ruwan dare gama duniya.
Malam Huseini Maiga shugaban masu dauke da cutar sida a kasar yace fatansu shi ne duk wanda yake dauke da cuta idan har ya ga likita to ya samu magani. Yace duk wani taimako da bai kaiga ba mutane magani ba, to bukatarsu bata biya ba. Yace su basu ce a basu kudi ba amma a sa likitoci su yi aikinsu su kuma bada maganin da ya cancanta.
Ga rahoton Abdullahi Maman Ahmadu.