Wadansu matasa, wa da kani, sun kwashe kwanaki goma sha daya suna tafiya da kafa tun daga Gamboru-Ngala dake jihar Borno zuwa Maiduguri babban birnin jihar. Daga Maiduguri suka nufi Kano kafin su tafi Maradi jihar Jamhuriyar Niger.
Matasan sun ce su 'yan asalin Niger ne amma basu san tushensu ba. Daya daga cikinsu Ibrahim Muhammed yace sun dawo daga Gamboru-Ngala domin dama can akwai 'yanuwansu a kasar Niger amma basu gane wajen 'yanuwan nasu ba. An kaisu yin makaranta ne a Gamboru-Ngala kafin 'yan Boko Haram su bata garin gaba daya. Da dare ya kama hannun kaninsa suka kama hanyar neman kasarsu.
Mahaifinsu yana kasar Sudan. Da ya barsu a makaranta sai ya tafi kasar Sudan domin iyayensa suna kasar. Da suke Gamboru-Ngala sukan samu labarin mahaifinsu amma yanzu babu.
Da matasan suka isa Maiduguri sun nufi tashar mota inda suka yiwa mutane bayani. Nan aka hada masu kudin aka sakasu cikin motar da ta kaisu Kano. Daga Kano kuma bisa ga bayanansu aka sake sasu a motar da ta kaisu Maradi.
Kawo yanzu dai basu san inda 'yanuwansu suke ba sai dai wasu sun fada masu sannu da hankali za'a ganosu. Yanzu dai yaran suna hannun ma'akata mai kula da yaran da suka shiga halin tagayyara.
Ga karin bayani.