WASHINGTON, D. C. - Sai dai bukukuwan ya ci karo da munanan ayyukan jin kai a zirin Gaza da kuma farmakin da ake sa ran Isra'ila za ta yi a birnin Rafah duk da kokarin da kawayenta na Yamma suka yi na dakatar da yakin bayan watanni shida na tsawon yakin.
A birnin Istanbul dubban masu ibada ne suka hallara a masallacin Aya Sofya domin gudanar da Sallar safiyar Idi, wasunsu dauke da tutocin Falasdinu suna rera taken nuna goyon baya ga al'ummar Gaza.
Da yawa sun ajiye dardumai na salla a dandalin da ke gaban tsohuwar babbar cocin Byzantine, wanda aka mayar da shi masallaci shekaru hudu da suka gabata, yayin da sarari a ciki ya cika da sauran mutane.
A cikin wani sakon biki, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya aike da tallafi zuwa Gaza, wanda ya kira "rauni mai zubar da jini a kan lamirin bil'adama."
Ya kara da cewa, "Ina fatan Idi zai kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da walwala ga kasarmu, al'ummarmu, duniyar Musulunci da dukkan bil'adama."
Haka an maida hankali kan yakin Gaza a addu’oin da aka yi a masallacin Rahma da ke Nairobi babban birnin kasar Kenya.
"Kada mu manta da 'yan uwanmu maza da mata a Palastinu," in ji Imam Abdulrahman Musa. "An zalunce su da cin zarafi ba gaira ba dalili kuma yawancin tashin hankali a yadda ga shi duniya tana kallo baki shiru."
A Indonesiya, al'ummar musulmi mafi yawan al'umma a duniya, kusan kashi uku cikin hudu na al'ummar kasar sun yi balaguro don dawowa gida na shekara-shekara da aka sani a cikin kasar a matsayin "mudik" wanda ko da yaushe ake maraba da farin ciki Idi.
Masu wa’azin a cikin wa’azin nasu sun yi kira ga jama’a da su yi wa musulmin Gaza addu’a da suke fama da su bayan yakin watanni shida.
Jimly Asshiddiqie, wanda ke shugabantar kwamitin ba da shawara na Majalisar masallacin Indonesiya ya ce "Wannan lokaci ne da ya kamata musulmi da wadanda ba musulmi ba su nuna hadin kai ga bil'adama, saboda rikicin Gaza ba yakin addini ba ne, illa ce ta matsalar jin kai."
Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim kuma ya yi kira ga hadin kai da sulhu a sakonsa na jajibirin Idi, yana mai cewa babu wata kungiya da za a mayar da ita saniyar ware saboda addini ko wani dalili.
-AP