Musayar Fursunoni Kashi Na 2 Tsakanin Hamas Da Isra'ila: An Sako Sojojin Isra'ila 4 Da Falasdinawa 200

Four Israeli female soldiers, Naama Levy, Liri Albag, Daniella Gilboa and Karina Ariev, are released as part of a ceasefire and a hostages-prisoners swap deal between Hamas and Israel, in Gaza City

Sojojin 4 mata na Isra'ila sun yi murmushi, tare da daga hannu da babban yatsa ga dimbin jama'ar da suka tattaru a wani dandalin Falasdinu a birnin Gaza. Hukumar gidan yarin Isra'ila ta sanar da cewa ta kammala sakin Falasdinawa 200.

Kungiyar Hamas ta saki sojojin Isra'ila hudu a jiya Assabar domin musanya da fursunoni 200 na Falasdinawa, a wani shiri na 2 na musayar fursunoni da wadanda ake garkuwa da su, a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.

Matan hudu sun yi murmushi, tare da daga hannu da daga babban yatsa ga dimbin jama'ar da suka tattaru a wani dandalin Falasdinu a birnin Gaza.

Akwai mayakan kungiyar da Amurka ta ayyana a matsayin ta ‘yan ta’adda a kowane bangare na su, kuma taron dubban jama'a ne suka kalla kafin sojojin na Isra'ila mata su hau motocin kungiyar agaji ta Red Cross da ke jira.

Masu lura da al'amura sun ce akwai yiyuwar mutanen hudun suna yin abubuwan ne bisa tursasa.

Wadanda aka yi garkuwa da su da aka saki a baya sun ce an tsare su ne a cikin matsanancin yanayi, kuma an tilasta musu yin hotunan bidiyo na farfaganda.

Hukumar gidan yarin Isra'ila ta sanar da cewa ta kammala sakin Falasdinawa 200. Hakan ya hada da mutane 120 da aka yanke musu hukuncin daurin rai da rai bayan an same su da laifin kai munanan hare-hare kan Isra’ilawa.

Kimanin mutane 70 ne aka sako a cikin kasar Masar, kamar yadda gidan talabijin din Qahera na kasar ta Masar ya bayyana.

Dubban Falasdinawa ne suka mamaye birnin Ramallah da ke yammacin gabar kogin Jordan don tarbon motocin safa da ke dauke da fursunonin, kuma da yawa daga ciki suna daga tutocin Falasdinu ko kuma tutocin bangarori daban-daban na siyasa.