A ziyarar da babban editan sasahen Hausa na Muryar Amurka, Alhaji Aliyu Mustapha, ke yi yanzu haka a Arewacin Najeriya ya yada zango a jihar Borno. Inda ya ziyarci wasu kafofin yada labarai don kokarin kulla zumunta.
Da farko ya fara ziyarar ne da gidan radiyon da ake kiransa Peace FM dake cikin garin Maiduguri, inda ya gana da manajan gidan radiyon Fatima Audu Yusuf, wadda ta nuna alfaharinta da irin wannan goron gayyata, da zai samar da kyakkyawar dangantaka ga kafofin yada labarun biyu.
Haka zalika wannan ziyara ta kai babban editan ga Kanem FM dake a jami’ar Maiduguri, wanda nan ma manajan gidan radiyon ke cewa wannan dama ce ta samu, ta watsa shirye-shiryen kafofin biyu da kuma damar samun horas da ma’aikata wajen kwarewa a aikin jarida.
Shima gidan talabijin na ‘kasa shiyyar Maiduguri NTA, ya karbi bakuncin jami’in Muryar Amurka. Alhaji Umar Lalo, dake zama manajan NTA Maiduguri, yace irin wannan yunkuri abin yabawa ne, kuma a shirye suke su karbe ta hannu bibbiyu.
Da yake bayani game da makasudin wannan ziyara da yake, Aliyu Mustapha, yace abubuwa uku ne na farko shine bukatar kulla dangantaka da kafofin watsa labarai domin samun cudanya ta yada shirye-shiryen kafofin. Na biyu, shine neman taimakawa Muryar Amurka wajen yayata wani shirinta na musamman na wasu hotunan bidiyo da ‘yan Boko Haram suka ‘dauka da kansu, dan wayar da kan al’umma na cewa akidarsu bata da alaka da musulunci. Sai kuma hada karfi da karfe wajen gudanar da shirye-shirye tare da sauran kafofin yada labarai.
Gwamanan jihar Borno Kashim Shettima, ya yabawa sashen Hausa na Muryar Amurka wajen watsa shirye-shiryen masu kayatarwa da fadakarwa dan kawo zaman lafiya ga al’umma.
Domin karin bayani ga rahotan Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5