Mahalarta taron sun tattauna kan yadda za'a shawo kan matsalar yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da satar shanu da kuma 'yan bindiga dake hallaka jama'a.
Jihar na fama da matsalolin tsaro a 'yan kwanakin nan inda mutane da dama suka rasa rayukansu tare da dukiyoyinsu, ko da yake hukumomi sun sha cewa suna iyakar kokarinsu wajen shawo kan lamarin.
Alhaji Huseni Boso mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya ya yi karin haske akan dalilin shirya taron. Ya ce sun kira taron ne domin su fadakar da jama'a cewa abun da ya faru ba su goyi bayansa ba. Ya kira bangarorin biyu da kada su yadda da wani ya zuga su domin su kona gidajensu.
Sun kira yaran Fulani matasa sun kuma fada masu cewa sace-sacen da su ke yi kungiyar Miyetti Allah ba ta yadda da hakan ba.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Neja Ardo Adamu Kaduna yace lamarin rashin zaman lafiya da ya addabi jihar ya ishesu. Ya kira shugabanni na al'umma da gwamnati da su taimaka su hada da addu'o'i basa son su sake jin wani tashin hankali. Yace zaman lafiya suke so.
Shugaban hadaddiyar kungiyar manoman jihar Neja Alhaji Shehu Galadiman Kontagora yace su manoma sun dauki taron da mahimmanci saboda ganin irin halin da kasar ta shiga baki daya.
Gwamnatin jihar ta ce za ta yi duk abun da ya wajaba domin tabbatar da dorewar zaman lafiya a tsakanin al'umma.
Brigadier Janar Abubakar Imam mai ritaya shi ne mai baiwa gwamnan jihar shawara akan harkokin tsaro kuma shi ya wakilci gwamnan jihar a taron. Ya basu shawara su fitar da duk wanda bashi da hali nagari. Idan kuma sun ga abun da basu yadda dashi ba su shaida masu, wato gwamnati.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Facebook Forum