Malam Sani Baga daya daga cikin magidanta kimanin arba’in, wadanda ke samun mafaka a yankin Hotoro, dake Kano, ya bayana yadda yaruwarsa ke fiya da ‘ya’yansa guda ashirin, yace har yanzu batun makarantar shike ci masu tuwo a kwarya.
Yanzu haka dai gamayyar ayarin ma’aikatan hukumomin bada agajin a Kano, guda shida wadandasuka hada da kungiyar Lafiya ta duniya da cibiyar yaki da yaduwar cututtuka ta Amurka, da kuma hukumar UNICEF, sun samarda tallafin abinci da magunguna da sauran kayayyakin masarufi ga ‘yan gudun hijiran.
Dr. Imam Wada Bello, babban jami’in cibiyar aikace aikacen gaggawa ta yaki da cutar Polio, a Kano shine ya jagoranci rarraba kayayyakin ga mabukatan.
Wani rahoto da ofishin cibiyar aiyukan jinkai ta Majalisar dinkin duniya a Najeriya, ya wallafa a makon jiya ya nuna cewa mutane fiye da miliyan biyar ne ke bukatar agaji bayan ta tarzomar Boko Haram, ta daidaitawa rayuwa a yakin arewa maso gabashin Najeriya.
Facebook Forum