Yace hakan na nufin maimakon su ciyar da kansu zasu cigaba da dogaro ga kasashen waje wajen samar ma al'ummominsu abinci.
Majalisar ta ECOWAS ta umurci kasashen su dinga bada kashi goma na kasafin kudinsu na kowace shekara kan harkokin noma. Wannan matakin da kungiyar ta dauka ya biyo bayan aikin wasu kwamitoci biyar da ta kafa wadanda suka yi aikinsu a kasar Senegal. Sun maida hankali ne kan karkata manufar ECOWAS a kan aikin gona.
Dr Huseni Hassan yace za'a iya cimma burin koda ba zasu iya bada kashi goma ba na kasafin kudinsu. Idan suka iya hada kashi biyar zai tallafa a wannan tafiyar da suka sa gaba. Hakan kuma zai shafi miliyoyin jama'a da za'a iya taimakawa. Yace za'a kuma iya korar yunwa.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum