Sanata Ndume yace “abunda ke da’akwai shine mu muna cikin tsaka mai wuya. Sau uku ana neman damar kafa dokar ta baci, mun yarda. Amma mai makon abun yayi kyau, abun kara tabarbarewa yake yi.”
“A yanzu da nake maka magana, kananan hukumomi kamar guda 10 suna hannun boko haram. Guda biyar a Adamawa, guda biyu a Yobe da kuma wasu kananan hukumomi a jihohin Bauci da Gombe wadanda ke zaman dar-dar”, a cewar Sanatan.
To ko majalisar dattawa zata iya hana shugaban kasa ayyana dokar ta baci.
Sanata Ndume ya kara da cewa “abunda kundun tsarin mulki ya fada shine sai majalisar tarayya tayi na’am, kuma yanzu majalisar wakilai na hutu.”
Muhammed Ali Ndume ya bayyana fahimtarsa game da yadda sojojin Najeriya da mayakan sa kai suke cigaba da kwam-gaba kwam-baya wajen kwato garuruwa a arewa maso gabashin Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5