Biyo bayan kwace jihohin Mubi da Maiha dake Jihar Adamawa, da ‘yan kato da gora suka yi daga hannun mayakan Boko Haram, lamarin da ya kara wa jama’a kwarin gwiwa game da kokarin kare kawunansu.
Al ummar Kaduna da kewaye, sun tofa albarkacin bakinsu game da furucin da Sarkin Kano yayi.
“Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi, Allah Ya kara mishi daukaka, yayi mana tuni akan abunda yi. Wajibi ne muna tsaron garuruwanmu, da kauyakunmu, da gonakinmu. Domin tsaro bana mutum daya bane. Tsaro na kowa ne, tunda jami’an tsaron nan basa iya tsare rayukanmu da dukiyoyinmu, wajibi ne mu kare kanmu,” a cewar wani mazaunin birnin Kaduna.
Wata mace cewa tayi “ina goyon bayan maganar Sarkin Kano, na cewa talakawa su fito su kare kansu. Ya kamata talakawa mu fito mu kare kanmu da kanmu.”
Mafi yawancin jama’ar da Sashen Hausa na Muryar Amurka yayi magana da su na goyon bayan tanadin da zai shirya jama’a su kare kawunansu, saboda gazawar jami’an tsaron Najeriya.