Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasancewa Borno Cikin Gwamnatin Tarayya ne Zai Kawo Karshen Tashin Hankali


PDP
PDP

Yayin da gwamnatin tarayya ke sabunta dokar ta baci a Borno, Yobe da Adamawa, karo na uku da ake sabunta dokar tsohon gwamnan jihar yace kasancewa cikin gwamnatin tarayya ne kadai zai kawo karshen fitinun.

Tsohon gwamnan Ali Modu Sheriff yayi jawabin ne a wani taron gangami da jam'iyyar PDP ta shirya a Maiduguri wanda ya samu halartar tsoffin ministocin Najeriya 'yan asalin jihar guda uku.

Ministocin sun hada da ministan wutar lantarki Barrister Mohammed Wakil.

Sanata Modu Sheriff ya soma da bayyana dalilansa na komawa cikin jam'iyyar PDP wadda ya kwashe shekaru goma yana adawa da ita. Yace a bisa ga tsarin Najeriya gwamnatin tarayya ce kadai zata iya kawowa jihar zaman lafiya da cigaba. Tun shekarar 1999 jihar ke adawa da gwamnatin tarayya lamarin da ya hanata samun cigaba.

Shi ma Barrister Muhammed Wakil ya kira 'yan jam'iyyar PDP da su zama 'yan uwa domin su cigaba da tafiyar. Yace tabbas za'a canza gwamnatin jihar ta koma PDP.

Alhaji Yusuf Adamu tsohon mai baiwa gwamna Kashim shawara akan harkokin siyasa yace sun canza sheka daga APC zauwa PDP domin su shiga tsakiyar siyasar Najeriya. Suna bukatar gwamnatin tarayya tayi masu hanyoyi, ta karbi makarantunsu na kimiya da kuma ganin an zauna an tallafawa mutane.

Alhaji Kassim Imam tsohon mai baiwa shugaba Obasanjo shawara ne kan harkokin 'yan majalisu wanda kuma yayi takarar kujerar gwamnan Bornn har sau uku yace sun yi babban kuskure da tallatar da gwamnan na yanzu domin ya kasa.

Duk da ikirarin da PDP keyi cewa gwamnan bai tabuka komi ba wasu al'umman jihar sun ce sun gani a kasa kuma sun shaida gwamnan yayi aiki. Duk da rashin tsaron da jihar ke fama dashi gwamnan bai taba kwana a waje ba. Idan ma yayi tafiya ya ji wani abu ya faru nan da nan zai koma jihar ya kuma je inda abun ya faru. Ana kone makaranta yana sake ginawa. Ana kone gidaje yana sake ginasu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:55 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG