Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa C P Sikiru Akande shi ne ya tabbatar da hakan a wurin wani taron maneman labarai da suka gudanar a helkwatar jihar.
Wakilin Sashen Hausa ya yi nasarar zantawa da wasu masu garkuwan, Tukur Adamu na daya daga cikin masu garkuwa da mutane a jihar Adamawa wanda kuma rundunar ‘yan sandan ta kama.
Ya ce dama wani makocinsa ne suka yi ma barazanar duka in bai basu kudi Naira dubu dari biyar ba, shi kuma ya je ya yiwa ‘yan banga bayani su kuma suka kama shi suka bawa ‘yan sandar jihar.
Bashiru Adamu wani tubabben dan garkuwa da mutane ne wanda kuma ya sake komawa cikin aikin kuma ya shiga hannu ‘yan sanda.
Shima cewa ya yi rabon a yine ya sake jefa shi cikin wannan aikin ama ya gane kuskuren shi kuma da yardan Allah ba zai kara ba kuma wannan ya zama na karshe a wannan aikin.
Sai dai Haruna Auwal ya ce zarginsa da ake yi da wannan aikin na garkuwa da mutane yasa ‘yan sandar saka kamo shi amma shi baya cikin masu wannan aikin.
Ga dai rahoton Lado Salisu Muhammad Garba daga Adamawa.
Your browser doesn’t support HTML5