Mun Kai Alhazai Dubu 25 Saudiyya Cikin Dubu 43 - NAHCON

NAHCON

NAHCON

Gabanin tsayuwar arfa ranar jumma'ar nan mai zuwa hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta ce alhazai dubu 25 cikin dubu 43 sun isa Saudiyya.

Wadannan alhazan sun hada da na jihohi dubu 33 da na jirgin yawo dubu 9 da 'yan kai.

NAHCON da ke amfani da kamfanonin jirage 3 biyu na gida daya na Saudiyya na nuna kwarin guiwar kammala jigilar gabanin rufewar karshe ranar laraba.

Tun a lahadin nan a ka rufe damar shigar jiragen alhazai Saudiyya in ka debe FLYNAS na Saudiyya da kuma kamfanin MAX da ya damu izinin cigaba da jigilar.

Ku Duba Wannan Ma Hukumar NAHCON Ta Shiga Yarjejeniya Da Masu Jiragen Sama Na Aikin Hajjin 2022

Jagoran kamfanin FLYNAS a Najeriya Umar Kaila ya ce za su yi duk abu mai yiwuwa wajen tabbatar dukkan alhazai sun samu sauke faralin a bana bayan dakatar da damar tsawon shekaru biyu a sanadiyyar cutar annoba.

Kaila ya nuna takaicin yanda jinkirin da a ka samu daga jigilar alhazan Abuja ya jawo tsaiko da kuma asarar kimanin dala miliyan daya ga kamfanin.

Jami'ar labarun alhazan Fatima Sanda Usara ta ce akwai tsarin da a ka yi bana don walwalar alhazan da kuma cigaba da samar da abinci irin na Najeriya.

Umar Kaila

Umar Kaila

A gaskiya bana da yawa masu niyyar zuwa hajjin sun kwance damara don rashin samun VISA da kuma karancin kujerun da a ka samu da su ka gaza bukatun jama'a.

Akwai mamaki yanda mutane su ka nace da zuwa hajjin bana duk da tsadar da kujerar ta yi mafi tsanani a tarihi da hakan ke nuna marmarin musulmi kan wannan babbar ibada.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Mun Kai Alhazai Dubu 25 Saudiyya Cikin Dubu 43 - NAHCON