Shugaban karamar hukumar Potiskum a jihar Yobe Salisu Muktari ya ce karamar hukumar ta dauki lauya don bin kadin yaron nan dalibi da wani babban dalibi ya yanka wuyansa da reza a kwalejin addinin musulunci ta El Kanemi da ke Maiduguri a jihar Bornon Najeriya.
Rahoto ya bayyana cewa shi babban dalibin ya sa yaron mai shekaru 11 mai suna Jubril Mato wani aiki ne da ya gaza gudanarwa sai ya yi amfani da reza ya yanka masa wuya har yaron ya fadi yayin da ya ke kokarin kai maganar wajen shugaban makarantar.
A labarin da ya sha bamban daga bakin shugaban karamar hukumar ta Potiskum Salisu Muktari, ya ce karamin yaron ya ga babban dalibin ne da wani abokinsa suna ludu, don haka babban dalibin ya yi yunkurin kashe yaron don kar ya tona masa asiri.
Zuwa yanzu an ba da labarin kama dalibin kuma yana hannun jami’an ‘yan sanda.
Salisu Mukhtari ya ce kasancewar yaron dan karamar hukumarsa ce, ya dau lauya don bin kadin yaron kuma zai yi tsayin daka sai an tabbatar da adalci.
Mukhtari ya bukaci gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya rufe kwalejin don gudanar da bincike kamar yadda gwamna Ganduje na Kano ya rufe makarantar “Noble Kids” don gudanar da binciken kisan gilla da aka yi wa wata yarinya mai suna Hanifa.
Sai dai tuni gwamnatin jihar ta Borno ta kafa kwamitin binciken lamarin kuma ana sa ran nan da kwanaki bakwai za su ba da rahoto kan wannan abin alhini da ya faru da Jubril Sadi Mato.