Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Hadin Kan 'Yan Arewacin Najeriya a Amurka Ta Agaza Wa Al'umma a Sokoto


 Kungiyar Zumunta ta kai agaji jihar Sokoto
Kungiyar Zumunta ta kai agaji jihar Sokoto

Kungiyar hadin kan 'yan arewa da ake kira Zumunta a Amurka ta tallafa wa al'ummomi da ibtila'in tashe-tashen hankula suka daidaita a jihar Sokoto.

Kungiyar Zumunta ta dauki wannan matakin ne tare da hadin gwiwa da kungiyar agaji ta Redcross reshen jihar Sakkwato, ganin yadda al'ummomi da dama a Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsin rayuwa a sansanonin da suke gudun hijira inda suke neman agaji.

A Najeriya musamman a yankin arewa dubban jama'a ne tashe-tashen hankula suka raba da gidajensu, wadanda ala tilas suka gudu suka bar komai dake gare su domin tsira da rayukansu.

Mafi yawa daga cikin su dake zaune a sansanonin yan gudun hijira suna cike da bukatu saboda yanayin da ya tilasta su baro gidajensu babu shiri.

Buhunan shinkafa da Kungiyar Zumunta ta kai agaji jihar Sokoto
Buhunan shinkafa da Kungiyar Zumunta ta kai agaji jihar Sokoto

A hirar shi da Muryar Amurka, Dahiru Masawa, hakimin wasu ‘yan gudun hijira da suka gudo daga garin Masawa a yankin Wurno na jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya, ya bayyana irin halin kunci da al'umma su ka shiga. Bisa ga cewarshi, 'yan bindiga suna aza masu kudin da za su rika basu a matsayin haraji, kuma bayan sun biya da 'yan kwanaki su sake dawowa. Yace sau da dama idan suka dawo sai su kwashe mata da kananan yara su tafi da su ya zama tilas suka bar garuruwansu suka koma sansanin 'yan gudun hijira.

Hakimin ya ce rayuwa ta zama da wuyar gaske a sansanin sabili da galibi basu da hanyar samun abinci ya zama da dama daga cikinsu sun zama mabaratan karfi da yaji don dole su nemi abinda za su ba iyalinsu su ci.

Duba da halin matsi da jama'a suke ciki da galibi matsalar rashin tsaro ta haifar yasa kungiyar ‘yan jihohin arewacin Najeriya mazauna kasar Amurka- Zumunta ,ta kuduri aniyar tallafa wa mabukata a Najeriya domin saukaka halin da suke ciki.

'Yan gudun hijira da Kungiyar Zumunta ta ba agajin shinkafa a jihar Sokoto
'Yan gudun hijira da Kungiyar Zumunta ta ba agajin shinkafa a jihar Sokoto

Wannan karon jihar Sakkwato na cikin Jihohin da suka amfana da tallafin inda kungiyar ta bai wa kungiyar bayar da agaji ta red Cross kudi domin taimaka wa jama'a kuma ta sayi buhuhuwan shinkafa 100 ta rabawa ‘yan gudun hijira dake yankin na Wurno.

A bayaninsa, Ibrahim Ngaski Sakataren kungiyar agaji ta Red Cross a jihar kebbi kuma wanda ya wakilci babban sakataren kungiyar na kasa, ya ce kamata ya yi kungiyoyi da daidaikun jama'a masu hali baiwa su yi koyi da kungiyar Zumunta domin taimaka wa dumbin mutanen da ke da matukar bukata.

Wannan tallafin na daga cikin jerin ayyukan jinkai da wannan kungiyar ke aiwatarwa ga ‘yan Najeriya domin saukakawa al'umma abinda jama'a da dama ke ganin cewa da sauran masu hali zasu yi koyi da hakan da an yayewa jama'ar kasar damuwa a fannoni rayuwa daban daban.

kungiyar-zumunta-ta-yan-arewacin-najeriya-tayi-taron-shekara-a-atlanta

hotunanliyafa-cika-shekaru-25-na-kungiyar-zumunta-wanda-uwargidan-shugaban-kasar-najeriya-hajia-aisha-buhari-ta-halarta-na-cika-shekaru-25-a-

An kafa kungiyar Zumunta a Amurka sama da shekaru kusan talatin da suka shige da nufin hada kan 'yan arewacin Najeriya mazauna Amurka da kuma hada hannu domin taimaka wa al'umma.

Kungiyar Zumunta ta gunar da ayyukan jinkai a jihohi dabam daban na kasar da suka hada da gina rijiyoyin burtsatse a jihohin arewacin kasar da dama da suka hada Adamawa, Borno, Filato, da Kaduna.

hotunan-bikin-taron-kungiyar-zumunta-na-cika-shekaru-25-a-amurka

Kungiyar tana tallafa wa dalibai masu karamin karfi da ke jami'o'in kasar, da kudi domin biyan kudin makaranta. Haka kuma kungiyar tana hada hannu da kungiyoyi masu zaman kansu da su ka yi fice wajen gudanar da ayyukan jinkai ta wajen tallafa masu da kudin gudanar da ayyukansu da suka hada da ba masu karamin karfi jari, da koya sana'oi da dai sauransu.

Saurari rahoton Muhammadu Nasir cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG