Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Yin Luguden Wuta Kan Birnin Maiduguri


Harin Boko Haram
Harin Boko Haram

Da alamar bakon da aka raka shi na neman ya dawo, saboda wasu da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun cillo abubuwa masu tarwatsewa, ciki har da masu kama da rokoki, kan birnin Maiduguri, inda aka ga barna sosai. Babu rasa rai amma.

A wani al’amari mai girgiza hanji, mutanen birnin Maiduguri a jihar Borno ta arewa maso gabashin Nijeriya sun wayi gari cikin tashin hankali na jin karar barin wutar da wasu da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram su ka yi ta yi babu kakkautawa, har da cillo wasu abubuwan da ake kyautata zaton rokoki ne, wadanda su ka fada kan gidaje su ka yi barna.

To amma duk da irin barnar da aka gani, musamman a unguwar Gomari Airport, ba a samu labarin rasa rai ba zuwa lokacin hada wannan rahoton. Hatta ruguza rukunin gidaje da rokokin su ka yi a unguwar One Thousand Unit, inda nan ma aka ga barna sosai, ba a samu labarin rasa rai ba zuwa lokacin hada rahoton.

Malam Kulima, wani da abubuwan fashewar su ka rushe wa gida, ya bayyana wa Muryar Amurka cewa bayan da ya dawo daga sallar asuba har ma bacci ya sake daukarsa, sai kawai ya ji karar bam, wuri ya turnike da kura, aka fara ihu a gidan, sai ya shiga dakuna ya kwashi iyalinsa.

Ya tabbatar da Muryar Amurka cewa, banda wata yarinyarsa da ta ji dan rauni, ba abin da ya samu kowa balle ma rasuwa. Amma y ace zuwa lokacin hada wannan rahoton, babau wata hukumar da ta tuntubi shi. Shi ma makwabcin Malam Kulima, wanda shi kuma gilasan gidansa ne su ka zube gaba daya, ya ce shi kuma ya na dawowa daga masallaci abun ya faru. Ya ce abin ya shafi gidajen mutane da dama, to amma babu wanda ya rasa ransa:

Saurari rahoton Haruna Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG