Mummunar Guguwar Michael Ta Afkawa Jihar Florida

Guguwar Michael

Jiya Laraba mahaukaciyar guguwar nan da aka radawa sunan Michael ta afkawa wani yankin jihar Florida, wadda ke zama guguwa mafi karfi a tarihi da ta taba afakawa doron ‘kasa a Amurka cikin shekaru 50.

Guguwar Micheal ta kai bakin teku ne akan kimar matakin hadari na 5. Gudun iskar guguwar ya kai kilimita 249 cikin sa’a, wanda yayi ta karkatar da ruwan saman dake kwarara.

Bishiyoyi da wayoyin lantarki sun fadi a fadin garuruwan dake yankin teku a Florida. Rufin gine-gine duk sun yaye. Manema labarai dake wajen da ta afkawa sunce sunji ‘karan taransfoma na wutar lantarki suna ta bindiga.

An tabbatar da mutuwar mutum guda sanadiyar guguwar. Wani mutum ya mutu bayan da bishiya ta fada kansa a garin Tallahassee.

Ya zuwa yammacin jiya Laraba guguwar Micheal tana tafiya da ‘karfin gaske, kuma ta koma mataki na 3 lokacin da ta nufi jihar Alabama da kudu maso yammacin jihar Georgia.

Jami’ai sunce duk mutanen da basu fice ba suke kan hanyar da guguwar ta nufa, su nemi mafaka.