Majalisar Dattawar Amurka ta amince da zaben Brett Kavanaugh a matsayin sabon alkalin kotun koli ta Amurka, bayan zargin da aka yi akanshi na yi ma wata mata fyade, tun a shekarun 1980, lokacin da suke makarantar sakandire.
Masana na ganin cewar Kavanaugh zai cike gurbin masu tsattsauran ra'ayi a cikin jerin alkalan kotun, wanda zasu zama 5 masu tsattauran ra'ayi, su kuma sauran 4 masu sassauci. Shi dai wannan matsayin na alkalin kotun koli wanda idan mutun ya kai gare shi, ba zai barshi ba har sai ya mutu.
Mr. Kavanaugh, mai shekaru 53 ka iya zama alkalin kotun na shekaru masu yawa. Shi dai alkali Kavanaugh ya maye gurbin Alkali Anthony Kennedy, wanda yake alkali na tara a kotun, an samu gurbi a kotun biyo bayan ritaya da yayi.
Jim kadan kamin jefa kuri’ar 'yan majalisun dokoki, shugaban Amurka Donald Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter cewar Alkali Brett Kavanaugh, zai zama alkali mai nagarta a kotun kolin Amurka.
Facebook Forum