Haley tsohuwar gwamnar jihar Carolina ta Kudu dake kudu maso gabashin Amurka, ta wakilci Amurka a Majalisar Dinkin Duniya tun lokacin da shugaba Trump ya hau karagar mulkin Amurka a shekarar 2017.
Haley ta yi kokarin kare manufofin gwamnatin Trump a kan Iran da kuma nuna goyon baya ga Isra’ila. Itace kuma ta shirya tafiyar Trump zuwa Majalisar Dinkin Duniya sau biyu, ciki har da jagorantar zaman kwamitin sulhu da yayi a karon farko.
Haley ta sanar da ajiye mukaminta a hukumance a jiya Talata a ofishin shugaban Amurka na Oval Office a fadar White House, yayin da take tare da shugaban kasa. Tace babu wani takamamman dalili a kan wannan murabus, sai dai tana gani lokaci ne ya yi.
Tace "ina ganin ina ganin yakamata jami’an gwamnati su san da cewa idan lokacin ajiye aiki ya kai babu makawa sais un ajiye, tace nayi iya bakin kokarina tsakanin shekaru takwas kuma ina gani lokaci ya yi da yakamata in baiwa wasu kuma dama su bada gudunmuwarsu".
Haley tace idan aka hada shekaru shida da tayi tana aikin gwamna, ta kwashe shekaru takwas tana yiwa kasa aiki kuma tace tana ganin ya isa haka.
Facebook Forum