Tsohon gwamnan jihar Imo kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar imo ta tsakiya, sanata Rochas Okorocha, ya bayyana cewa idan ya sami shugabancin Najeriya za’a sami zaman lafiya da hadin kai a Najeriya.
Rochas ya bayyana hakan ne a birnin tarama Abuja a yayin wata hira ta musamman inda ya ce shi dan siyasa ne da ya riga ya yi aiki a lokutan baya. Ya ce, ba ya daga cikin 'yan siyasa da su ke ikirarin za su yi aiki saboda ga ayyukan da ya yi birjik a kasa ana gani.
A cewarsa Rochas, 'yan siyasa a zamanın yanzu idan suka tashi gangamin yakin neman zabe cewa suke zasu yi aiki kaza da kaza amma shi ba ya fadin haka saboda ya riga ya yi su aikace a baya an gani. Ya na mai cewa a kusan duk sassan Najeriya ciki har da yankunan arewa maso yamma, gabas da tsakiya, kudu da yammaci akwai aikin da Rochas ya yi a bayyane.
Rochas dai ya kara da cewa a halin da Najeriya ke ciki, 'yan kasa na bukatar shugaba mai tausayin jama’a da suka hada da talakawa, marasa galihu, mai tausayin marayu da dai sauransu.
A cewarsa, ya na da alaka da talakawan kasar ta fuskoki da dama musamman a gidauniyar Rochas inda ya ke daukan nauyin karatun dubban ‘ya’yan marasa karfi kuma idan ya sami shugabancin Najeriya, zai kara kaimi wajen kula da ilimin 'yan kasar.
Haka kuma, Rochas ya ce shi cikakken dan kasuwa ne kuma la’akari da albarkatun kasa da Najeriya ke da su ya na mai cewa daga sakkwato zuwa jihar Kwara gwal ne ake da su jibge a karkashin kasa amma ba basirar a fito da su don amafani ga 'yan kasar su sami ayyukan yi musamman ga matasa.
Rochas ya ce idan ‘yan Najeriya suka ba shi damar shugabanci, zai gyara ababe muhimmai uku da suka hada da amfani da albarkatun kasar yadda ya kamata wajen cigaba, farfado da tattalin arzikin kasar, kawo karshen talauci da rashin ilimi wanda yace su ne ginshiki wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar a yanzu.
Kasar Najeriya ba ta rasa komi ba kawai rashin basirar sarrafa albarkatun da Allah ya ba wa kasar shi ne babu kuma ya kamata a mayar da hankali wajen mai ilimi da basirar da za’a farfado da fannin ilimi da tada komadar trttalin arzikin kasar, in ji Rochas.
Ku Duba Wannan Ma Yadda EFCC Ta Gurfanar Da Rochas Jim Kadan Bayan Ayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Zaben 2023Kazalika, Rochas ya ce da tsaro da talauci kaman mata da miji su ke, gado daya su ke kwana kuma idan ba’a gyara daya ba dayan kuma ba zai gyaru ba. Bisa ga cewar sa, duk inda ka ga talauci za’a sami rashin tsaro da zubda jini don yunwa ake fama da su.
A game da tsarin karba-karba, Rochas ya ce kamata ya yi a yi adalci ba maganar karba-karba ba saidai ya ce an tsaida Najeriya kan kafa uku ne da suka hada da ‘yan kabilun igbo, yarbawa da Hausa/Fulani kuma Yarbawa da Hausawa sun ja ragamar mulkin kasar na tsawon lokaci amma 'yan kabalar Igbo ba su yi ba, ya kamata a yi adalci.
Idan aka duba ta fuskar dimokuraddiya, Rochas ya ce mutane masu mafi yawan jama’a zasu ci gaba da mulkar Najeriya kamata ya yi a yi adalci dai domin samun zaman lafiya.
Rochas dai ya kara da cewa ya cancanci a ba shi dama ya mulki Najeriya don zai mayar da hankali wajen kawar da talauci, bunkasa tattalin arziki, samawa matasa ayyukan yi da dai suuran muhimman abubuwa.
A yayin amsa tambaya kan gurfanar da shi bisa zargin wawure kudadden al’ummar jihar Imo a lokacin da ya yi gwamna, Okorocha ya ce tun da ya sauka daga mulki a ke yi masa bita da kulli amma har yanzu ba’a same shi da lifin komai ba sai dai hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ki mutunta umarnin kotu na ta daina yi masa bita da kullin tare da kin biyan diyyar naira miliyan da wata babbar kotu ta umarci ta biya shi.
Rochas ya ce kamar yadda mutane ke cewa akwai hannun siyasa a zargin da EFCC ke ma sa duba da yadda ta gurfanar da shi a gaban wata kotu a ranar da ya bayyana aniyarsa ta neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya a makwannin baya.
Sai dai a matanin da ya bayar dangane da wannan zargin, shugaban hukumar EFCC ya ce ba bita da kulli ake yiwa Rochas ba illa lokaci ya yi bayan sun gudanar da bincike su gurfanar da shi a gaban kotu, kuma kotu ce kawai zata iya tabbatar da mai laifi.
Saurari cikakkiyar hirar ta musamman da Sanata Rochas Okorocha kan neman takarar shugabancin Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5