WASHINGTON D C —
A wannan makon ne hukumar jarabawar shiga jami’a da makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta jaddada tabbacin fara sayar da takardun zana jarabawar ta bana, wato shekarar 2017.
Hukumar ta kuma fitar da wasu muhimman bayanai da zasu kara wayar da kan dalibain da zasu zana jarabawar a wannan shekara masu matukar amfani.
Ga kwararan matakai 10 da kowane dalibi ya kamata a sani kamar yadda mujallar Daily Trust ta wallafa:
- Za a sayar da takardun zana jarabawar wato (Forms) na tsawon wata guda ne kacal, kuma za a fara sayar da shi ranar 20, ga watan Maris, a kammala ranar 19, ga watan Afrilu.
- Za a sayar da (FORM) din a kan kudi Naira 5,500. Kuma ya kumshi komi da komi harda kudin rajista da jaddawalin karatu wato (Brochure)
- Za a rufe rajistar jarabawar ranar 22, ga watan Afirilu, 2017.
- A bangaren dalibai masu bukatar takardun shiga jami’a ki tsaye wato (Direct Entry) kuma, za a fara sayar da (FORM) daga ranar Lahadi 23, ga watan Afrilu, 2017.
- Za a zauna jarabawar (JAMB) a ranar 6, da kuma ranar 20, ga watan Yuni, 2017.
- Ba za a zana jarabawar a ranar 12, ga watan Mayu ba domin a ba daliban dake zana jarabawar kammala karatun sakandire, (WAEC) damar zana jarabawar (Futher Mathematics).
- Daliban da ke jiran sakamakon jarabawar gaba da sakandire na iya zana jarabawar JAMB, amma su tabbatar suna da sakamakon jarabawarsu a hannu yayin za a fara bada takardun izinin shiga jami’a.
- Daliban da suka yi rajistar jarawar JAMB MOCK, zasu zana jarabawar a ranar 8, ga watan Afrilu.
- Cibiyoyin CBT, zasu iya cajinkudi har Naira 700, na jarabawar Mock.
- An samar da sama da cibiyoyi 600 na zana jarabawar a duk fadin Najeriya.