Wannan ne jigon bukatar iyayen da 'yan gwagwarmayar ceto matan BBOG a taron tunawa da cika shekaru 10 da sace matan da a ka gudanar a Abuja.
Gangamin da ya gudana a dandalin UNITY ya samu halartar jigogin neman sako matan irin su tsohuwar minista Oby Ezekwesili, Dr.Emman Shehu, Aisha Yesufu da sauran su da su ka jagoranci karanta sunayen mata 82 da su ka rage a hannun 'yan ta'adda.
"Mu na bukatar barranta da neman afuwa ga duk iyaye da al'ummar Chibok don barin wasu daga cikin 'ya'yan su na zama tare da wasu tubabbun 'yan ta'adda da gwamnatin Borno ta bar su su ke cewa su mazajen su ne." Inji babban shugaban al'ummar Chibok na duniya Dauda Iliya.
Nan take jagora kuma daya daga iyayen matan Nkeki Mutah ya ce sam ba su amince su aurar da 'ya'yansu ga 'yan Boko Haram ba "ba mu yarda da tubansu ba. Mu abun da mu ke so dama gwamnati ta yi ma na shi ne ta bincika yaya wani irin aure ne su ke ikirari. Fyade ne ba karamin fyade ba ma. "
Rabecca Samuel da 'yarta Sarah ba ta dawo ba ta ce gara a samu matan ko wani mataki za a dauka.
'Yan kungiyar BBOG irin su Amina Aliyu Usman da Injiniya Shehu Abubakar na karfafa ba su debe tsammanin samo sauran matan ba.
Taron ya tabbatar iyaye biyu sun saduda da bayan gano 'ya'yansu sun mutu inda a BBOG kuma a ka yi addu'a ga 'yan kungiya 15 da su ka mutu a tsawon shekarun 10 ciki kuma da jagoran 'yan Chibok a Abuja Sambido Hosea da a ka ce ciwon zuciyar rashin ceto dukkan matan ya zama sanadiyyar mutuwarsa a 2021.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5