Ceton yazo ne shekaru tara bayan da ‘yan ta’addar kungiyar Boko Haram suka kai hari tare da sace ‘yan mata 276 lokacin da suke rubuta jarabawar kammala sakandare a makarantar garin Chibok.
Sojojin sun sami nasarar ceto ‘yan matan a wani yanki na Boko Haram dake dajin Sambisa, da suka bayyana sunayensu da Esther Marcus da Hauwa Malta, dukkanninsu shekarunsu 26 da haihuwa.
A cewar rundunar, an ceto Esther tare da jaririyarta mai shekara guda. Kuma ta yi aure har sau uku ga ‘yan kungiyar da suke garkuwa da ita.
Haka kuma an ceto Hauwa Malta da cikin wata takwas, kuma ta haifi yaro a cibiyar da aka ajiyesu ake kula da su kwanaki 10 bayan ceto su.
Sojojin sun kuma kashe sama da mutane 70 da ake zargin ‘yan ta’adda ne a farmakin da suka kai a yankin Arewa maso Gabas.
Adadin 'yan matan da aka ceto yanzu ya kai 125, ciki har da 107 da 'yan ta'addan suka sako a shekarar 2018, uku da sojoji suka ceto a shekarar 2019, biyu a 2021, da 11 a 2022.
Domin Karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.