Wannan ya biyo bayan matakin da shugabar babbar kotun tarayya Monica Dongban Mensem ta dauka na takaita yanke kararrakin a biranen biyu.
Shugabar kotun daukaka karar ta dau matakin bayan yawaitar korafi daga kotunan karar zabe da ke nuna rashin gamsuwa da hukunce-hukunce da a ka yanke don yiwuwar cusa kan wasu 'yan siyasa.
Tun dawo da daukaka kara zuwa Abuja, an sami shari'un da a ka soke daga hukuncin da kotunan zabe su ka yi da su ka shafi majalisar dattawa da wakilai.
Lauya mai zaman kan sa a Abuja Barista Modibbo Bakari ya ce matakin na da tasiri don tsaurara hanyar isa ga Alkalan. "Za ka ga masaukan baki na alkalan zaben na hannun gwamnoni ne don haka za'a iya samun shishshigin 'yan siyasa."
Shi ma Barista Zakariya Mu'azu ya ce tsarin dokar gaggauta yanke hukuncin kotun daukaka kara na taimakawa a wannan bangare.
Tuni wasu daga cikin 'yan takarar gwamna da ba su yi nasara ba a kotun karar zabe irin gwamnan Nasarawa A.A Sule da na Kano Abba Kabir Yusuf su ka daukaka kara.
Kazalika 'yan takara ma da ba sa kujera irin su Farfesa Sani Yahaya na NNPP a jihar Taraba sun daukaka kara don rashin gamsuwa da hukuncin kotun karar zabe.
Kotun koli, a na ta bangaren, za ta fara sauraron daukaka karar kalubalantar aiyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe ranar Litinin mai zuwa bisa daukaka kara da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Leba su ka yi.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5