Mu Ma Mun Fuskanci Irin Wannan Yanayi A Najeriya – Hukumar Kwallon Kafa Ta Libya

'Yan wasan Najeriya na Super Eagles (Hoto: Facebook/Super Eagles)

A ranar Litinin, kungiyar kwallon kafa ta maza ta Najeriya ta janye daga wasan da za a yi a Libya, inda ta nuna fushinta kan yadda aka yashe su a filin jirgin sama bayan da aka karkata akalar tafiyarsu

Hukumar Kwallon Kafa ta Libya (LFF) ta soki matakin da Najeriya ta dauka na janyewa daga wasan neman cancantar shiga gasar AFCON ta 2025 da za a buga a Libya, kuma tana barazanar daukar matakin shari'a.

A ranar Litinin, kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, ta bar wasan tana mai yin nuni da damuwar tsaro bayan da aka bar su a filin jirgin sama na Al-Abraq a Libya ba tare da abinci ko intanet ba har na fiye da awa 16.

A cikin sanarwar da Hukumar Kwallon Kafa ta Libya (LFF) ta fitar a ranar Talata, ta zargi takwararta ta Najeriya, wato Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), da nuna rashin hadin kai da masu shirya wasan na cikin gida.

LFF ta ce karkatar da jirgin zai iya zama sakamakon tsare-tsaren jirgin sama na yau da kullum, binciken tsaro ko matsalolin dabaru da ba a iya shawo kansu ba.

Ta kara da cewa 'yan wasan Libya ma sun fuskanci irin wadannan matsaloli a wasannin baya da aka buga a Najeriya.

LFF ta ce za ta dauki dukkan matakan shari’a don kare muradun kungiyar kwallon kafa ta kasar Libya.

A ranar Litinin, kungiyar kwallon kafa ta maza ta Najeriya ta janye daga wasan da za a yi a Libya, inda ta nuna fushinta kan yadda aka yashe su a filin jirgin sama bayan da aka karkata akalar tafiyarsu.

NFF ta ce an kai kungiyar zuwa filin jirgin sama na Al-Abraq, wanda yake nisan awa uku daga filin wasan, kuma hukumomin yankin ba su samar da wasu shirye-shiryen tafiya ga kungiyar ba.