Adamu Maina Waziri ya bayyana raayin sa game da danbaruwar dake faruwa a cikin majilisar dokokin Najeriya sailin da suka tattauna da Bello Habeeb Galadanchi.
Yana mai cewa wannan abu fa dole a fuskance akan siyace kuma shi siyasa a yadda yakamata a fahinta shine baka da masoyi na din din din haka kuma baka da makiyi na din din din, sai dai biyan bukatar ka shine abinda zaka yi ta fafitikar nema an wayi gari mu PDP munyi haarar shugaban kasa da Gwamnatin tarayya da ainihin jihohi ana neman a nuna kamar an gama damu sai muka samu da sukuni domin ALLAH ba azalumin kowa bane muka samu dan kofa muka sa tsohon dan PDP ya zama shughaban majilisar dattijai muka sad an PDPmaici ya zama mataimakin shugaban majilisar dattijai’’.
Wato zargin da yan jamiyyar APC keyi na cewa kuka kitsa duk wadannan abubuwa haka ne?
‘’Ai siyasa ce koba mu muka yi ba ma mu muka yi dama a siyasa idan akayi maka shairi sai kayi janhuru yanzu abinda suka yi muna a APC sun kwace muna gwamnatin tarayya da sauran wurare mu kuma mun musu janhuru mun kwace makjilisar dattijai’’.
To yanzu abinda su yan APC suke yi suna da shige daku abinda kuka rage a baya musammam a majilisun nan?.
‘’A ai na fada kwanan baya cewa mu PDP zamu yi hamayya bana tsangwamma ba, hamayya na hankali na natsuwa shi zamu yi yanzu, kumaMallam Rabiu Musa Kwankwaso kwananan ya bar PDP fa’’
Kace Kwanan ya bar PDP?
‘’A Mallam Musa Kwankwaso kwanan nan ya bar PDP, Danjuma Goje kwanan ya bar PDP da yake koke koke duk wannan abu kawai abu ne na siyasa na samun fage’’.
Zaku jawo Bukola SAraki ya dawo PDP?
‘’Ai Bukola Saraki dan PDP ne a yanzu, dan PDP wadanda zamu jawo sune irin su Mallam Rabiu Musa Kwankwaso da ire-iren su wadanda har yanzu suna da kayan baya su zamu jawo amma su amma Bukola Saraki dan PDP ne’’
Bello Habeeb Galadanchi ne yayi hirar.
Your browser doesn’t support HTML5