Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AME Charleston: Masu Sujada Sun Yi Dafifi Jiya Lahadi


Mijami'ar Emanuel AME dake Charlestonjihar South Carolina inda wani fara fata Dylan Roof ya kashe mutane tara makon jiya
Mijami'ar Emanuel AME dake Charlestonjihar South Carolina inda wani fara fata Dylan Roof ya kashe mutane tara makon jiya

A karon farko tun bayan da wani farar fata ya kai hari kan majami'ar nan mai dumbin tarihi a jihar South Carolina cikin makon jiya, har ya kashe mutane tara, jiya Lahadi, masu ibada sun dunguma zuwa cocin domin ibada.

Da kakkausar murya Rev Norvel Goff shine maye gurbin shugaban majami'ar na wucin gadi, ganin Clementa Pickney wanda shine jagoran majami'ar yana daga cikin mutane taran da aka kashe ranar Laraba da ta shige.

Rev Goff, yayi kira ga daruruwan mutanen da suka halarci cocin cewa, su dogara da Allah yayinda suke ci gaba da jimamin wadanda suka mutu.

Masu ziyara ga cocin daga sassan garin na Charleston, da kuma wasu daga wurare kamar jihar California ne suka cika majami'ar. Lokacin ibadar wasu 'yan agaji suna rabawa mutane ruwa, da mafifici saboda zafin cikin cocin ganin ana fama da bazara yanzu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG