Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Yobe: An Hana Wasu Ma'aikata Albashinsu


Alhaji Ibrahim Geidam gwamnan jihar Yobe
Alhaji Ibrahim Geidam gwamnan jihar Yobe

Wasu ma'aikata a kananan hukumomi shida dake jihar Yobe sun yi kukan rashin biyansu albashi tun bayan zaben watan Afirilu saboda basu zabi gwamna Ibrahim Geidam ba.

Ma'aikatan sun ce shugabannin mulki a kananan hukumomin shida sun bada umurnin a rike masu albashi bisa zargin cewa basu zabi jam'iyyar gwamnati ba ko kuma gwmna Ibrahim Geidam. Korafin ya fito fili ne a taron zauren dattawan jihar Yobe mazauna Kano.

Wani da aka zanta dashi yace yana aiki a karamar hukumar Karasuwa ta jihar Yobe kuma yanzu yana cikin wata uku da ba'a biyashi albashi ba. Yace a wajen zaben gwamna na 11 ga watan Afirilu an sa masu ma'aikata masu sa ido su duba su ga wadanda basu zabi gwamnatin jihar ba saboda arike albashinsu. Duk wadanda basu zabi gwmna Ibrahim Geidam ba su ne suka shiga tarkon rike albashinsu.

Kawo yanzu akwai kimanin mutane dari da tamanin da suka shiga wannan tarko na gwamnatin jihar Yobe. Ma'aikatan sun cigaba da zuwa aiki amma babu alamun za'a biyasu. Wani da shi ma ba'a biyashi ba yace a nashi sanin kuma a matsayinsa na dan kasa yana da cikakken 'yanci ya zabi kowacce jam'iyya yake so ba tare da tsangwama ba.

Dangane da haka zauren dattawan 'yan asalin jihar Yobe dake Kano ya kira gwamnatin jihar da ta sanya baki cikin batun. Alhaji Habu Dauda Gurami shugaban zauren ya kira gwamnatin jihar ta matsawa wadannan kananan hukumomi shida da su biya ma'aikatan.

Shugaban ma'aikatan kananan hukumomin Najeriya reshen jihar Yobe Kwamred Musa Hassan El-Badawi yace sun yi zama da shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar kuma yace idan akwai irin wadannan mutane a tattara sunayensu a kai masa. Yace suna bi su tabbatar an warware matsalar. Yace matsalar ta siyasa ce. Shugabanninsu na wadan nan kananan hukumomin ke da matsala. A tsakaninsu suke yin wadannan abubuwa.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG