Motocin Dakon Kaya A Iyakar Nijar Sun Koma Najeriya Da Kayansu

Motocin dakon kaya akan ikayar Nijar da Najeriya sun juya suka koma

Matakin rufe iyakokin ya kawo cunkoson manyan motoci makare da kaya wadanda ke son shiga Nijar amma babu dama.

ABUJA, NIGERIA - Rahotanni daga kan wasu iyakokin Najeriya na cewa motocin dakon kaya da dama na komawa kasar sakamakon rufe kan iyakoki da Jamhuriyar Nijar.

Hukumomin Najeriya sun ba jama'a hakuri kan wannan mataki da aka dauka wanda suka ce na dan wani lokaci ne.

Mukaddashin Shugaban Hukumar hana fasa-kwauri, Bashir Adewole Adeniyi, ne ya sanar da haka lokacin da yake zagayen iyakokin na Najeriya da Nijar domin tabbatar da suna rufe.

Duk da yake jagororin Gwamnatin soji ta Jamhuriyar Nijar tuni sun bude iyakokin kasar da wasu kasashe da ke makwabtaka da ita da suka hada da Mali, Chadi, Burkina Faso, Libya da Algeria, iyakokinta da Najeriya har yanzu suna rufe.

Wannan yanayin dai tuni ya haifar da koma-baya ga hada-hadar kasuwanci da cudanyar mutanen kasashen biyu.

Iyakar Najeriya da Nijar

A wani mataki mai nuna Gwamnatin Najeriya tana kan bakarta ta tabbatar da ci gaba da rufe iyakokin bisa ga matakin Kungiyar ECOWAS, Gwamnatin ta bayar da hakuri akan illolin da rufe iyakokin ya haifar.

Mukaddashin Shugaban Hukumar hana fasa-kwabri Bashir Adewole Adeniyi ya ce matakin na wuccin gadi ne duk da yake ba zai rasa kawo radadi ga wasu ba.

Ya ce babu abin da za'a ce ya fi zaman lafiya, "muna son a samu zaman lafiya a Nijar da ma duk kasashen da ke Nahiyar ta Afirka, amma wannan matakin an dauke shi ne domin tabbatuwar karfafa dimokradiya a Nijar da Najeriya da ma dukkan kasashen yankin."

A cewarsa harkokin kasuwanci za su samu ci gaba ne kawai idan da zaman lafiya, amma idan ba zaman lafiya kuma akasin haka za'a samu, don haka ana son fara samun zaman lafiya kafin ci gaban kasuwanci.

Wannan matakin na rufe iyakokin ya kawo cunkoson manyan motoci makare da kaya wadanda ke son shiga Nijar amma ba dama, duk da yake da yawa cikin su, sun sallama sun dawo cikin Najeriya.

Yanzu da yake wa'adin da kungiyar ECOWAS ta bayar ga Gwamnatin sojin Nijar ya cika, da yawa mutanen kasashen yankin sun zura ido ganin yadda zata kaya.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Motocin Dakon Kaya A Iyakar Nijar Sun Koma Najeriya Da Kayansu.MP3