MohBad: Majalisar Wakilan Najeriya Ta Gayyaci Naira Marley

Hoton marigayi MohBad yayin wani gangamin tunawa da shi da aka yi a Legas.

Ana sa ran mawakan biyu da aka gayyata za su bayyana ne a gaban kwamitin majalisar a ranar Talata mai zuwa.

Majalisar Wakilan Najeriya a ranar Alhamis ta mika takardar gayyata ga Azeez Fashola wanda aka fi sani da Naira Marley.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa matakin gayyatar mawakin, kokari ne na tattala wa da killace kudaden shiga da MohBad ke samu, wanda asalin sunansa Ilerioluwa Aloba.

Kwamitin tabbatar da adalci da kula da lamurran matasa a majalisar, ta kuma gayyaci mawaki Jiggy Adeoye don ya je a tattauna da shi.

Ana sa ran mawakan biyu da aka gayyata za su bayyana ne a gaban kwamitin majalisar a ranar Talatar mako mai zuwa.

A ranar 12 ga watan Satumbar 2023 MohBad wanda da yaron Naira Marley ne a karkashin kamfaninsa na Marlians ya rasu yana mai shekaru 27.

Jaridar Premium Times ta yanar gizo ta ruwaito cewa Majalisar wakilan ta dauki matakin gayyatar mawakan biyu ne bayan da dan majalisa Babajimi Benson na jam’iyyar APC daga jihar Legas ya gabatar da bukatar hakan.

Mutuwar ta MohBad ta zo ne bakatatan ta kuma wakana ne cikin wani yanayi mai cike da rudani, lamarin da ya sa har yanzu 'yan sanda ke rike da Naira Marley da wasu mutane da ake zargin suna da hannu a mutuwarsa.