Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mohbad: Zan Koma Najeriya Idan ‘Yan sanda Za Su Ba Ni Kariya – Naira Marley


Naira Marley (Instagram/Naira Marley)
Naira Marley (Instagram/Naira Marley)

Jama’a da dama na ta dora alhakin mutuwar Mohbad akan Naira Marley wanda shi ne tsohon maigidansa da ya fara daukansa a aiki a kamfaninsa na Marlians. Naira Marley ya musanta zargin.

Fitaccen mawakin Afrobeat a Najeriya, Azeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley, ya ce a shirye yake ya koma kasar idan har ‘yan sanda za su ba shi cikakkiyar kariya.

“Dari bisa dari, zan koma Najeriya idan ‘yan sanda za su ba ni kariya.” Naira Marley ya ce yayin wata tattaunawa da suka yi da Reno Omokri, tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara.

"Zan je don na wanke kaina," Naira Marley ya kara da cewa.

Naira Marley ya shiga tsaka mai wuya tun bayan mutuwar tsohon yaronsa Ilerioluwa Oladimiji Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.

Mohbad mai shekaru 27, ya rasu a ranar 12 ga watan Satumba cikin wani irin yanayi mai cike da rudani a Legas.

Jama’a da dama sun yi ta dora alhakin mutuwar Mohbad akan Naira Marley wanda shi ne tsohon maigidansa da ya fara daukansa a aiki a kamfaninsa na Marlians.

Mohbad da Naira Marley sun samu sabani a bara, lamarin da ya sa Mohbad ya bar kamfanin. Rahotanni sun ce hakan bai yi wa Naira Marley dadi ba.

Sama da mutum dubu 300 sun dena bin Naira Marley a shafinsa na Instagram ciki har da fitattun mawakan Najeriya saboda zarginsa da hannu a mutuwar mawakin.

Kalaman Naira Marley na zuwa ne bayan da ya fitar da wata tattaunawa ta bidiyo da suka yi da Mohbad inda yake rarrashin matashin mawakin kan yunkurin da yake yi na kashe kansa.

MohBad
MohBad

Cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, Mohbad ya ambaci cewa idan ya mutu Naira Marley ne sanadi.

Shi dai Naira Marley ya musanta hannu a mutuwar Mohbad tun bayan aukuwar lamarin mai cike da sarkakiya.

A makon jiya ‘yan sanda suka tono gawar Mohbad don a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwarsa.

Jami’an tsaro rike da wata ma’akaciyar jinya da ake zargin ta yi masa wata allura saboda wani rashin lafiya. Jim kadan bayan allurar Mohbad ya rasu.

Bayanai sun yi nuni da cewa Naira Marley da mukarrabansa da suka hada da wani yaronsa mai suna Sam Larry sun hana Mohbad sakat inda suka yi ta bibiyar duk inda yake don su muzguna masa.

Naira Marley da Larry wadanda yanzu ba a san inda suke ba, sun musanta wadannan zarge-zarge.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG