Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MohBad: ‘Yan sandan Legas sun Kama Sam Larry


Sam Larry
Sam Larry

Naira Marley da Sam Larry sun sha musanta hannu a mutuwar MohBad, wanda ya rasu cikin wani yanayi mai sarkakiya.

‘Yan sandan jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya sun ce suna tsare da Balogun Olamilekan, wanda aka fi sani da Sam Larry.

Sam Larry, wanda na hannun daman mawaki Azeez Fashola da aka fi sani da Naira Marley ne, na daya daga cikin mutanen da ake zargin sun taka rawa wajen mutuwar matashin mawaki Ilerioluwa Oldimeji Aloba da aka fi sani da MohBad.

“Balogun Olamilekan Eletu da aka fi sani da Sam Larry ya shiga hannunmu. Yanzu haka yana taimakawa ‘yan sanda a binciken da ake kan yi.” Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta sanar a shafinta na Facebook a daren Alhamis.

Naira Marley da Sam Larry sun sha musanta hannu a mutuwar MohBad, wanda ya rasu cikin wani yanayi mai sarkakiya.

Rahotanni sun nuna cewa sabani ya shiga tsakanin Naira Marley da MohBad ne, tun bayan da shi MohBad ya fice a kamfanin Marlians na Naira Marley a bara, lamarin da bai yi wa Naira Marley dadi ba.

Bayanai sun yi nuni da cewa, tun da MohBad ya fice a kamfanin wasu da ake zargin yaran Naira Marley ne ciki har da Sam Larry suke ta bibiyarsa suna cin zarafinsa, zargin da suka musanta.

A makon da ya gabata aka tono gawar MohBad wanda ya mutu yana da shekaru 27 don gudanar da bincike kan musabbanin mutuwarsa.

MohBad
MohBad

Matashin mawakin ya rasu ne a ranar 12 ga watan Satumba bayan da wata ma’akaciyar jinya wacce yanzu haka take hannun hukuma, ta yi masa wata allura.

Jama’a da dama a ciki da wajen Najeriya, ciki har da fitattun mawaka irinsu Davido, Zlatan da Falz sun halarci gangamin neman a hukunta wadanda ke da hannu a mutuwar MohBad.

An yi zanga-zanga da dama cikin makon da ya gabata a jihohin kudancin Najeriya don neman a bi wa MohBad kadinsa.

Kama Sam Larry da ‘yan sandan suka yi, na zuwa ne kwana guda bayan da Naira Marley ya ce a shirye yake ya koma Najeriya don ya wanke kansa idan har ‘yan sanda za su ba shi kariya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG