Majalisar zartaswar kasar Yamal ta koma gida daga gudun hijira da ta soma yayin da 'yan tawayen Houthi suka mamaye fadar shugaban kasar lamarin da ya yi sanadiyar yaki da kasar ta fada ciki
WASHINGTON DC —
Kakakin gwamnatin kasar Yamal yace Ministocin kasar sun dawo daga gudun hijira bayan kwashe watanni a kasar Saudi Arabia.
Ministocin za su yi zaman tsara dawo da daidaiton al’amura a birnin Aden da ke gabar tekun kudancin kasar.
Kamar yadda Kakakin ya fada a jiya Laraba majalisar zartsawar kasar ta dawo. To sai dai babu wasu alamun dawowar shugaban Kasar Abdu Rabu Mansour Hadi.
Shugaban ya sulale daga kasar ne a farkon shekarar nan bayan ‘yan tawayen Houthi sun datse birnin Aden.
A jiya Laraba Amurka ta sanarda karin wasu Dala Miliyan Tamanin da Tara na taimakon Yamal da abinci, ruwan sha, magunguna da matsuguni.