Ministar Kudin Najeriya Ta Mikawa Majalisun Kasar Kasafin Kudin Badi

Ministar Kudin Najeriya Ngozi Okonjo Iweala

Sau uku shugaban kasar Najeriya ya dage kai kasafin kudin badi gaban majalisun kasar domin banbancin da suka samu kan farashin da za'a sayar da gangaar danyan man fetur
Takaddama kan kudin da za'a sayar da gangar danyan man fetur ya sa shugaban kasar ya dage gabatar da kasafin kudin badi har sau uku. A wannan karon ma ministar kudi ce ta mikawa majalisun ba tare da yin wani bayani ba.

Ministar kudin Najeriya Ngozi Okonjo Iweala ta shiga zauren taron majalisun biyu inda ta mika kasafin kudin kuma ta fita cikin mintuna talatin kacal. Sai dai yayin da ta gana da manema labarai a harabar ginin majalisar ta yiwa 'yan jarida bayanin abubuwan da kudun kasafin kudin ya kunsa.Ta ce kasafin kudin na nera tiriliyon hudu ne da biliyon dari shida.Manyan ayyuka zasu ci tiriliyon daya da biliyon daya ko kashi 27 cikin dari na kasafin kudin kana kananan ayyuka zasu ci kashi 72 cikin dari na kasafin kudin.

Sanata Abubakar Totari ya ce abu ne da ba'a taba yi ba amma an fara shi yau. An saba shugaban kasa shi yake kawo kasafin kudi amma yau ministar kudin ta kawo kodayake hakan bai saba ma kaidar doka ba amma a bisa ga cancanta da yakamata shugaban ya kawo ma majalisun kamar yadda aka saba.Ya ce a wannan karon an kawo kasafin a dunkule an ajiye. Su basu san abubuwan dake ciki ba domin babu bayani. Hatta shugaban majalisar dattawa bai san abun dake cikin kasafin ba. Abun bakin ciki kuma shi ne ministar kudin ta zo ranar da majalisun zasu rufe su tafi hutun karshen shekara.

Amma tsohuwar ministar kudi Sanata Nenadi Esther Usman ta ce kawo kasafin ya yi mata dadi domin an dai kawo. Karshenta za'a aikawa kowane sanata ya karanta. Don haka babu wata matsala. Shi kuwa Ahmed Babba Kaita dan majalisar wakilai daga jam'iyyar adawa ta APC ya ce su basu daukeshi kasafin kudi ba tukunna. Zasu bude su ga idan ya dace da abubuwan da talakan Najeriya ke bukata zasu yi 'yan wasu gyare-gyare su bari ya wuce. Idan kuma bai dace ba to gaskiya akwai rigima.

A ra'ayin Sanato Babayo Gamawa ya ce hakin majalisun ne su binciki yadda aka yi anfani da kasafin kudi kuma duk kwamitocinsu zasu bincika. Idan an bada kudi a yi hanya a tabbatar an yi hanyar. Idan kuma ba'a yi ba laifi ne kuma zasu dauki matakan da suka dace bisa ga abun da kundun tsarin mulki ya tanada.

Ga Medina Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ministar Kudin Najeriya ta Mikawa Majalisun Kasar Kasafin Kudin Badi - 3:48