Hajiya Kadija Kasum shugabar tawagar ta babban bankin ta bayyana makasudin ziyararsu. Ta ce suna jihar ne su wayar da kawunan jama'ar jihar musamman masu hulda da bankuna. Abu na biye da wannan shi ne su karfafa masu gwuiwa su cigaba da yin hulda da bankuna kuma su gaya masu hakoki da suke dasu a bankunan da ma hakokin da bankuna suke da shi. Idan suna da koke akwai inda zasu iya kaiwa. Hajiya Kasum ta ce akwai babbar kofa da aka bude da zasu iya zuwa a babban bankin Najeriya su shigar da kokensu.
Dangane da wasu bankuna dake cutar jama'a Hajiya ta ce akwai hanyoyi da yawa da ake tantance bankuna. Duk bankin da babban banki ya bashi takardar izinin kafashi suna sane da shi kuma dole ne ya bi kai'dodin da aka bashi. Amma wani abun da ya sa suka kawo ziyara Jos shi ne su wayar da kawunan jama'a su guji hulda da bankunan wuru-wuru.Yawancin irin wadannan bankunan sukan yiwa mutane tayin kudin ruwa mai yawa da zasu biya kan ajiyar da aka basu. To amma fa idan da kwadayi to da wulakanci. Hajiya ta kira mutanen Filato da ma 'yan Najeriya gaba daya su guji irin mutanen dake shafa masu romon banza a baki.
Idan aka gano mutane masu yin wuru-wuru akwai sashi na babban banki inda za'a kai kara su kuma nan da nan zasu kamasu su mikasu ga mahukunta.Da aka fada mata cewa akwai wasu da suka aikata wuru-wuru a Jos inda suka yi anfani da bankin da babban banki ya amince da shi suka damfari mutane amma har yanzu ba'a kamasu ba kuma suna cikin garin Jos.
Kan bankuna da ke cigaba da cire ma mutane kudi bayan sun gama biyan rancen da suka karba sa Hajiya ta ce idan mutum ya karbi bashi ya kamata ya tambaya wata nawa zai yi yana biya, kuma kudin ruwa nawa ne domin ya san idan ya gama biya ya gama. Duk wani kudi kuma da aka cire bayan ya gama biya ya zama cuta. Idan kuma banki ya debe fiye da abun da ya kamata dole mutum ya tambayi dalilin yin hakan. Idan mutum bai gamsu ba ya ruwa zuwa babban banki.
Babban bankin zai yiwa duk ma'akatan banki bita tukunna. Dga bisani kuma ya yiwa masu hulda da bankuna da za'a gayyato har ma daga karkara a yi masu bita a harshen da zasu gane inda za'a yi masu bayanai dalla-dalla.
Zainab Babaji nada karin bayani.