Da take jawabi ma kwamitin majalisar dattawa dake sa ido kan yadda ake kashe kudin shirin SURE-P Ngozi Okonjo Iweala ta ce wadannan zunzurutun kudi da aka tara domin tallafawa shirin SURE-P din nera biliyan dari takwasne da goma sha shida sai aka karkasasu tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi da na kananan hukumomi domin samar ma al'umma abubuwan more rayuwa da zasu kawo masu saukin rayuwar yau da kullum.
Alhaji Bukar Ali Satoma shugaban kwamitin tsare- tsare na kwamitin SURE-P ya ce an dora masu shirye shirye da ayyukan gine-gine da ake bukata cikin gaggawa. Ayyukan da aka dora masu na musamman ne idan kuma babu su babu cigaba. Wadannan sun hada da gina hanyoyi da gadoji da gina layin dogo. Akwai kuma shirya ayyukan yi na matasa da mata, wato koyan ayyukan sana'o'i da wadannan zasu yi anfani dasu su samu abun rayuwa. Akwai shiri na nakasassu da masu aikin kiwon lafiya da na ngozoma. Duk wadannan ana basu tallafi.
Shugaban kwamitin bincike Sanata Abdul Ningi ya ce bincike ya zama wajibi domin ana maimaita ayyukan ne. Ya ce ana ninka kudade ne kan aiki daya. Misali idan an dauki kudin SURE-P an gina hanya to yakamata a banbantashi da kudin kasafin kudin da aka sa za'a gina wannan hanyar. Wato ko a yi anfani da kudin kasafi a gina hanyar kana a karkata kudin SURE-P da sunan gina wannan hanyar. Ba za'a ce an dauki kudin SURE-P an saka an gina hanya daya an kuma dauki kudin kasafin kasar an saka a wannan aikin hanyar to ina kudin SURE-P ya shiga ko kudin kasafin. Idan babu wannan banbancin to aikin banza ne domin wasu kudi sun salwanta. A wata hanya a Neja Delta gwamnatin tarayya ta sa kudi a kanta hukumar Neja Delta ita ma ta sa kana aka ce an sa kudin SURE-P to me aka yi kenan. Ta yaya za'a gane wane kudi aka yi anfani da shi aka gina ahanyar.
Shi kwamitin SURE-P ya kamata a ce duk lita daya na mai da aka sayar yana da nera 33 da zai tara domin tallafawa talakawan Najeriya.
Medina Dauda nada karin bayani.