Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya ruwaito hukumomi na cewa an sace mutanen ne da yammacin ranar Jumma’a a jihar Edo ta kudancin kasar. Jami’an sun ce mutane ukun na hanyarsu ta zuwa Benin, hedikwatar jihar Edo don shirye-shiryen auren diyar alkalin yayin da ‘yan bindigar su ka tsaida motarsu.
Rahotannin sun ce wadanda suka sace mutanen ba su tuntubi iyalin Alkalin Kotun Koli Bode Rhodes-Vivour don gabatar da wata bukata ba.
Sace-sacen fitattun mutane sun karu a kudancin Nijeriya a ‘yan watannin nan, ta yadda akasarin lokaci masu sace mutanen kan bukaci kudaden fansa daga iyalan mutanen da su ka sacen.
A watan Disamba ma, an sace mahaifiyar Ministar Kudin Nijeriya Ngozi Okonjo-Iweala a jihar Delta kafin aka sako ta bayan kwanaki 5. Ba a bayyana ko an biya kudin fansa ba.
Garkuwa da mutane dai ta zama sana’a mai kawo kudi sosai ga bitsararru a kudancin Nijeriya, to amma a shekarun da su ka gabata, akasarin al’amarin na shafar ‘yan kasashen waje ne da ke aiki da kamfanonin mai.