Ministar harkokin kudin Faransa Christine Lagarde, ta bayyana niyyarta ta takarar shugabancin asusun bada lamuni na duniya IMF duk da kiraye kirayen da ake yi na bada shugabancin asusun ga wata kasa da bata turai ba. Christine Lagarde tana cikin manyan ‘yan takarar shugabancin asusun, bayanda tsohon shugaban kungiyar Dominique Strauss Khan yayi murabus makon jiya sakamakon zargin tilastawa wata ma’akaciyar O’tel lalata da shi. Yau laraba Lagarde ta bada sanarwar zata nemi wannan mukami. Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai karkashin jagorancin shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel sun bayyana karara cewa, suna son wani dan kasar Turai ya shugabanci hukumar bada lamunin ta duniya a lokacin da take taimakon kasar Girka da Ireland da kuma Portugal shawo kan matsalolin bashi da suka dabaibaye su. Sai dai kasashe masu tashen arziki suna kushewa kane-kane da kasashen Turai suka yi da shugabancin IMF. A cikin sanarwar hadin guiwa tsakanin Brazil da Rasha da India da China da kuma Afrika ta Kudu sun ce lokaci ya yi da za a sake akidar nacewa sai wani daga kasashen Turai zai shugabanci bankin bada lamunin na duniya.
Ministar kudi ta kasar Faransa ta bayyana niyarta ta neman shugabancin asusun bada lamuni na duniya-IMF
Ministar harkokin kudin Faransa Christine Lagards, ta bayyana niyyarta ta takarar shugabancin asusun bada lamuni na duniya IMF duk da kiraye kirayen da ake yi na bada shugabancin asusun ga wata kasa da bata turai ba.