Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Misra Za Ta Bude Kan Iyakarta Da Zirin Gaza

Firayim Ministan Misra kenan Essam Sharaf
Firayim Ministan Misra kenan Essam Sharaf

Gwamnatin Misra ta ce za ta bude kan iyakarta da Zirin Gaza da ke karkashin ikon Hamas daga ranar Asabar mai zuwa dindindin, wanda zai kawo karshen killacewar da aka yi wa zirin na tsawon shekaru 4 inda kimanin Falasdinawa miliyan 1 da dubu dari 4 ke zaune.

Kamfanin dillancin labaran Misra MENA ya fadi jiya Laraba cewa Maketarar Rafah, wadda it ace kawai maketara ta halal daga Israila zuwa cikin Gaza—za a cigaba da kula da ita ne bisa tsarin da ake amfani das hi kafin killacewar da aka yi a 2007.

Wato daga ranar Asabar mai zuwa duk wani ba-Falasdine mai Passfo zai iya ketarawa zuwa cikin Misra kullu yaumin imbanda ranar Jumma’a da ranar hutu. Mata za su iya fita daga Gaza ba tare da wani sharadi ba a sa’ilinda su kuma maza ‘yan shekaru 18 zuwa 40 za a bukace su su mallaki Visar kasar Misra a kan iyakar.

Kamfanin Dillacin Labaran na MENA y ace wanna na daga cikin kokarin kara dankon zumunci tsakanin Falasdinwa da kuma sasanta su. A watan jiya ne Misra ta daidaita tsakanin kungiyar Fata da shugabna Mahmoud Abbas da ta hamas wanda ya kawo karshen jayayyar tsawon shekaru hudu.

Da Israila da Misra sun rufe kan iyakokinsu da zirin Gaza a 2007 bayan da mayakan Hamas suka mamaye zirin.

XS
SM
MD
LG